21 Maris 2026 - 15:27
Source: ABNA24
Tel Aviv: An kai wa Jirgin Yaƙinmu Hari A Sararin Samaniyar Iran 

Sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa an kaiwa wani jirgin yaƙinsu hari da makami mai linzami a saman sararin samaniyar Iran. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: bisa nakaltowa daga shafin Annashr, sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa an kai wa daya daga cikin jiragen yaƙinta hari a sararin samaniyar Iran; Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa, wani makami mai linzami da ake har ba shi daga ƙasa zuwa ya kai wa daya daga cikin jiragen yaƙinta hari a sararin samaniyar Iran.

 Sojojin wannan gwamnati ba su yi karin bayani akan lamarin ba.

............

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha